Dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Sergio ya haɗe da kungiyar Barcelona ta lasar Spaniya bayan da Kwantiraginsa ya kare a karshen kakar bana.
Dan wasan dan kasar Argentina mai shekara 32 ya bar City ne bayan shafe shekara goma yana murza mata leda.
Gabannin bankwana da kungiyar, Aguero ya kasance dan wasan Manchester City da ya fi kowanne zura mata kwallo bayan da ya ci kwallaye 260 cikin wasanni 390 da ya buga.
Wasan karshe da Aguero ya bugawa City shine wanda ya shigo a benci a karawar karshe ta gasar zakarun turai sa Chelsea ta lashe a ranar asabar din da ta gabata bayan ta doke Manchester City 1:0.
“Mun san cewa Barcelona ita ce babbar kungiya ɗaya tilo a duniya da ta fi kowacce” Cewar Aguero.
“Ina ganin na yi kyakkyawan tunani na kasancewa a nan Nou Camp, ba makawa wannan wani mataki ne na inganta harkar tamaulata”
Yanzu haka dan wasan zai shafe shekara biyu ne a kungiyar wato daga yanzu har zuwa farkon shekara ta 2024 kenan.