Mahaifin Lionel Messi da wakilinsa, Jorge, sun gana da shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu, wanda ya shaida musu cewa ba zai sayar da dan wasan Argentina, mai shekara 33 ba kamar yadda Marca ta labarto.
Ganawar farko da aka yi tun bayan Messi ya nemi barin Barcelona ta tashi baram-baram, inda kungiyar ta ce dole ya kammala kwangilarsa ta shekara biyu inji Mundo Deportivo.
Kudin da Barcelona za ta karba idan Messi zai bar kungiyar zai iya zama kasa da Yuro miliyan 100 in ji jaridar Telegraph.