A gasar kofin Zakarun Turai da aka buga a wannan tsakiyar makon nan, kungiyar Barcelona dake kasar Sipaniya, ta tashi kunnen doki wato 0 da 0 da kungiyar Salva Praha ta kasar Czech Republic.
Duk da kunnen dokin da Barcelona ta yi da Salva Praha, sai dai har yanzu Barcelona din ne ke ci gaba da jan ragamar rukuninsu na F a kofin gasar Zakarun Turai din. Duk da Dortmund ta yi nasara kan Inter Milan da ci 3 da 2, hakan bai bai wa Dortmund din darewa saman Barcelona ba, amma tashi kunnen doki da Barcelona ta yi da Salva Praha, barazana ce ga kungiyar. Kuma hakan na nuni akwai bukatar kungiyar ta tashi tsaye wajen ganin ta rika cimma nasara a wasanninta.
A kaftanin wasan na jiya Talata, kungiyar Salva Praha ta ki yadda ta yi sanyi balle ta bai wa Barcelona kofar yin nasara akanta, a yayin da ita kuma Barcelona ta dage domin ganin ta yi nasara kan kungiyar, lamarin da ya kai wankin hula zuwa dare.