Mai Martaba Sarkin Katagum na Jihar Bauchi Alhaji Umar Kabir Umar na biyu ya naɗa Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde a matsayin Barden Yamman Katagum.
A Jiya Alhamis ne dai Mai Martabar ya mika wa gwamnan wannan sarauta a yayin wata ziyarar kaddamar da ayyuka da ya je izuwa Jihar ta Bauchi bayan da gwamnan Jihar Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya gayyace shi.
Wannan sarauta tana zuwa ne kwanaki biyu bayan da Mai Martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya yi makamanciyar ta ga Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan inda ya nada Shi matsayin Jigon Bauchi, sarauta da ta janyo Cece kuce a faɗin kasar nan.
Wasu daga cikin al’umma na ta nuna jin daɗin su game da sarautun biyu inda suke cewa sun chanchancu hakan duba da irin namijin ƙoƙarin su a kasar nan, yayin da wani bangare ke ganin sarautun kamata ya yi a ce sun zamo na yan yankin ne.
Idan za a iya tunawa dai Gwamnan Jihar Bauchi ya kasance Ministan Birnin Tarayya Abuja Karkashin Mulkin tsohon shugaba Jonathan, yayin da alakar shi da Makinde kuma ta kasance ta siyasa a jam’iyyance.