By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, ya jajantawa iyalan wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai ya rutsa dasu a barikin Bataliya ta daya ta Dukku da ke Birnin Kebbi.
Gwamnan ya bayyana ta’aziyyarsa ne a ranar Juma’a a lokacin da ya halarci addu’o’i na musamman a babban masallacin bariki domin samun zaman lafiya da wadanda harin ya rutsa da su.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa, Bagudu ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar Babale Umar-Yauri, da mukaddashin shugaban ma’aikata, Alhaji Sufyanu Garba-Bena, da wasu jami’an gwamnati.
Gwamnan ya ce ya je barikin ne domin yin ta’aziyya da kuma gudanar da addu’o’i na musamman ga wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su, da jiga-jigan sojoji da ’yan banga da suka rasa rayukansu.
Bagudu ya kuma jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da kuma wadanda suka samu raunuka daban-daban, ya yi fatan samun sauki a gare su.
Ya ce “Muna nan kan abin bakin ciki don jajanta wa juna, kan kalubalen da aka fuskanta a ‘yan kwanakin da suka gabata da dai sauransu, da dama daga cikin jami’an tsaro sun rasa rayukansu.
“Don haka a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kebbi muna jajantawa tare da yi wa wadanda suka rasa rayukansu addu’a.
“A matsayinmu na Musulmi da Kirista dukkanmu mun yi imani da kaddara. Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan Allah ya kaddara, muna addu’ar Allah ya kawar mana da faruwar lamarin nan gaba .
“Muna addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu kuma muna sake tausayawa iyalansu.
“Muna addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kebbi da Najeriya baki daya.”
Bagudu ya bukaci jama’a da su jajanta wa iyalan wadanda suka rasu ta hanyar taimakawa musamman zawarawa da marayu da ke tsakaninsu.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa hukumomin tsaro karkashin kulawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari za su maido da zaman lafiya a yankunan da ake fama da rikici a kasar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa babban limamin masallacin Barikin na Dukku, Imam Mukhtar Muhammad, ya yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a kasar nan da kuma duk wadanda suka mutu a harin da aka kai a Kanya da ke karamar hukumar Danko Wasagu.
Limamin ya nemi taimakon Allah don kare dukkan ‘yan Najeriya tare da tallafa wa jami’an tsaro wajen samun nasara kan munanan ayyukan ‘yan bindiga.
Ya kuma yabawa gwamnan bisa ga irin kulawar da yake baiwa iyalan sojojin da aka kashe a fadin jihar.
A ranar Alhamis ne Bagudu ya umarci masallatai da coci-coci da su gudanar da addu’o’i na musamman a ranakun Juma’a da Lahadi, biyo bayan kashe-kashen da ‘yan bindiga suka yi a wani bangare na masarautar Zuru.