By Abbas Yakubu Yaura
Dangane da yadda gobarar data tashi a dakunan kwanan dalibai, hukumar gudanarwar jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta hana daliban dake zaune a gidajen kwanan dalibai yin girki a cikin dakunansu.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa kimanin gobara uku ce aka samu a makwannin da suka gabata a gidajen kwanan dalibai da suka yi sanadin jikkata da hasarar dukiyoyi masu yawa.
Hukumomin makarantar sun ce gobarar data tashi ta tashine sakamakon murhun dafa abinci.
Wata takardar dake dauke da sa hannun shugaban dalibai Farfesa A.M. Gimba mai taken: “Sanarwar Gargaɗi akan dafa abinci a dakuna,” tace za a kori ɗaliban da suka yi kasa a gwiwa wajen bijirewa wannan umarni daga ɗakin kwanan dalibai.
“A ‘yan kwanakin nan jami’ar tafuskanci tashin gobara a dakunan kwanan dalibai, musamman ma a dakunan kwanan dalibai mata.
“Wannan yana da nasaba da dafa abinci a dakuna wanda ya sabawa ka’idojin zama na masaukin dalibai.” in ji shi.
Gimba yace an dauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyin daliban, inda yace mahukuntan jami’ar sun umurci jami’an zaure da su tabbatar da dakile afkuwar irin haka ta hanyar korar duk wani dalibi da aka samu yana girki a dakin.
Sai dai kuma “Duk wani yunƙuri na ɗalibi ko ƙungiyar ɗalibai na cin zarafi ko kawo cikas ga duk wani memba na ma’aikaci wajen sauke nauyin daya rataya a wuyansa ya kai ga rashin da’a wanda zai haifar da fitar da shi daga Jami’ar.”