By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an sako wani basaraken gargajiya na yankin Umuezeala-Ama mai cin gashin kansa a karamar hukumar Ehime Mbano ta jihar Imo, Aloy Igwe.
Idan za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An yi garkuwa da basaraken ne a ranar 14 ga watan Disamba.
An saki sarkin ne a yammacin ranar Laraba, kamar yadda wata majiya data nemi a sakaya sunanta ta bayyana.
Kazalika an yi garkuwa da basaraken ne a lokacin da yake tattaunawa da mutanensa a kasuwar Nkwo-Umuezeala kwanaki biyu bayan da aka yi garkuwa da wasu sarakunan gargajiya biyu, Acho Ndukwe da Paul Ogbu daga yankin Ihube masu cin gashin kansu tare da lalata musu gidaje da kuma kone motocinsu.