Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga Naira tiriliyan 41.60 (dala biliyan 100.07) a watan Maris zuwa Naira tiriliyan 42.84 (dala biliyan 103.31) a watan Yuni.
Ofishin kula da basussuka (DMO) karkashin jagorancin Patience Oniha ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau Talata.
Jimillar basussukan yana wakiltar hannun jarin cikin gida da na waje na Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Duk da cewa bashin da ake bin kasashen waje ya kasance Naira Tiriliyan 16.61 (dala biliyan 39.96), bangaren gida ya karu zuwa Naira Tiriliyan 26.23 (dala biliyan 63.24).
KARANTA ANAN: An Yiwa Mai Gadin Kasuwar Jos Yankan Rago
Ofishinta ya lura cewa sama da kashi 58 cikin 100 na hannun jarin bashin waje na rancen rangwame ne.
An samo su ne daga Bankin Duniya, Asusun Ba da Lamuni na Duniya, Afrexim da Bankin Raya Afirka, da kasashe da suka hada da Jamus, China, Japan, Indiya da Faransa.
Adadin bashin cikin gida ya haura daga Naira tiriliyan 24.98 (dala biliyan 60.1) a watan Maris zuwa Naira tiriliyan 26.23 (dala biliyan 63.24) a watan Yuni.
Wannan ya biyo bayan rancen da Gwamnatin Tarayya ta yi don cike gibin kasafin kudin 2022, da kuma sabbin rancen da gwamnatocin jihohi da FCT suka yi.
A wani labarin kuma: Ku tabbatar anyi Zaɓen 2023 cikin Zaman Lafiya – Kiran Limamai ga Ƴan Siyasa
Majalisar Limamai da Malamai reshen Jihar Kaduna, ta yi kira ga ƴan siyasa da Musulmi baki daya da su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali ba tare da nuna kyama ba, a daidai lokacin da ake fara yakin neman zaben 2023.
Mataimakin Babban Sakatare-Janar Imam Musa Tanimu da jami’in hulda da jama’a na majalisar, Dokta Abdullahi Maikudi, a wani taron Manema Labarai na haɗin gwiwa, jiya a Kaduna, sun kuma yi kira ga ‘yan kasar da su guji maganganun da ka iya haifar da karya doka da oda.