Tsohon Mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci wata babbar Kotu dake birnin tarayya Abuja da ta vbyi watsi da karar da aka shigar kan cewa a haramta mishi tsayawa takarar shugabancin kasa a shekara ta 2023.
Alhaji Atiku Abubakar wanda shine ya fafata gurmuzun neman shugabancin kasa na babbar zaben da ya gabata ya ce karar da wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa ta shigar babu sanin zafin kai a cikin ta.
Cikin Wata takarda da Nanchang Ndam ya shigar gaban kotun wanda dake kalubalantar karar da aka kai Atiku ta ce babu abin da karar za ta haifar face bata wa kotu lokaci.
Baya ga Atiku dai yayin zamar, akwai wasu da ake kara da suka hada da Jam’iyyar PDP, Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta (INEC) da kuma Atoni Janar na tarayya.
Lauyan Mai shigar da kara ya gabatar da wasu tambayoyi da suka hada da “Shin ko sashe na 25 na kundin tsarin mulkin shekara ta 1999 da aka yi wa gyaran fuska ya ce lallai sai an haifi mutum ne a kasa kafin yake zama cikakken dan kasa”?
“Ko Kuma sashe na 131 (a) na kundin tsarin mulkin Najeriyar ya ayyana cewa lallai sai wanda aka haife shi a kasa ne kawai zai tsaya takarar shugabancin kasar Najeriya”?
Bisa Wadannan tambayoyi ne dai ya sa Lauyan mai shigar da karar ya bukaci kotun ta fayyace wa jama’a yadda kundin tsarin mulki ya bayyana cewa haifaffen dan kasa ne kadai ke da damar tsayawa takara.
To sai dai a wata takarda hadin gwiwa da Jam’iyar PDP da Atiku suka gabatar, ta bayyana cewa iyayen Atiku, Kakannin da Kakannin Kakannin shi ma duk yan Najeriya ne kuma sun gushe suna a matsayin yan Najeriya, don haka babu wani wanda ke da hurumin bayyana shi a matsayin wanda ba dan Najeriya ba.