Wata kotu a Kano ta aike da Abdulmalik Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan yari, bayan da aka zarge shi, da kalaman bata suna ga gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Kotun dai ta yanke masa hukuncin zama a gidan yari har zuwa 15 ga watan Maris, inda za a sake dawo da shi kotun, domin ci gaba da sauraran shari’ar tasa.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bata suna da tunzura al’umma.
Ana tuhumarsa da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka baiwa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jam’iyyar
Comments 1