A yanzu haka dai cece-kuce da rade-radi sun yi nisan zango a jihar Zamfara game da tsohon gwamnan jihar Abdul’Aziz Yari inda ake zarginsa da karkatar da kudin gwamnati da kimaminsu ya kai biliyan 60.
A lokacin Mulkinsa Yari ya samu dama fiye da kowanne gwamna da jihar Zamfara ta taba, inda ya yi karfa-karfa kan wasu al’amura da suka shafi jihar.
Duk da irin koma bayan da ya samu na faduwa zabe, Yari na cigaba da yunkuri wajen ganin ya dawo kan ganiyarsa ta neman sake samun wata damar zai mulki jihar.
A cikin wannan yanayi da ake ciki na fatar da talauci, tsohon gwamnan yayi amfani da wannan dama wajen sayan kayan abinci sama da tirela 300 inda ya rabawa mabukata a fadin jihar.
Amma duk da irin wannan hali na kulawa da yake nunawa jihar ta Zamfara bai tsallake rijiya, a yayin da aka yamutsa hazo bayan da tsohon Ministan sufurin Jirage, Femi Fani Kayode ya tona asirin tsohon gwamnan a shafinsa na Twitter.

Kayode, ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya bada kwangilar biliyan 60 ga wani kamfanin ‘yan China kuma an cire kudin tun kafin a fara dasa harsashin aikin.
https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-zamfara-ta-fara-raba-naira-biliyan-shida-ga-matasa/
Amma gwamnati mai ci ta yanzu karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bukaci kamfanin da su sabunta kwantiragin ko kuma su dawo da kudin da adadinsu ya kai biliyan 60.
Amma abun tambayar a nan shi ne duk da irin Karfi iko da tsohon gwamnan yake da shin hukumar yaki da almundahana ta jihar zata iya hukunta shi ko kuwa?.

Daga daya bangaren kuwa ‘yan jam’iyayyar adawa na dada hura wutar cewa ba kamata a bar Yari yake yawo yadda ya kamata ba, ya kamata hukuma ta tuhume sa don sanin ina kudin suka kwana.
Mutanen jihar Zamfara ba zasu manta da irin gudunmawar da Yari ya samu daga wajen tsohon maigidansa ba kafin ya zama abinda ya zama a yau.
A lokacin da Sanata Ahmed Sani Yarima ya mulki jihar daga shekara ta 1999 zuwa 2007, ya nada Yari Sekataren gwamnati, wanda daga bisani ya nada shi shugaban jam’iyyar ANPP, sannan ya sake bashi tikitin dan takarar majalisar wakilan tarayya.
Haka zalika, a shekara ta 2011 Yarima ya sake amfani da ikonsa wajen tunbuke Aliyu Mahmuda Shinkafi daga takarar gwamna ya bawa Abdul’Aziz Yari.