Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, yayi ƙarin haske kan sa labulen da yayi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
An yi ta kace-nace dai tun bayan da aka ga Ganduje ya raka Shekarau zuwa gidan sa bayan sun je sallar jana’izar babban ɗan kwangila, Alhaji Sani Dahiru Yakasai (SDY), a fadar sarkin Kano, ranar Juma’a.
KU KARANTA KUMA: Ga irinta nan: Budurwa ta koka bayan saurayinta ya ƙi karɓar cikin da ya ɗirka mata
A yayin da wasu masu sharhi ke kallon hakan a matsayin siyasa ce, wasu na ganin cewa Shekarau na iya sanya magoya bayan sa su zaɓi ɗan takarr gwamnan Kano na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Nasir Gawuna, a zaɓen ranar Asabar dake tafe.
Sai dai, a wata hira da gidan rediyon Faransa (rfi), Shekarau wanda ɗan jam’iyyar PDP ne kuma ɗaya daga cikin darektocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar yace ganawar ta su ba siyasa bace.
A kalamansa:
“Maganar gaskiya itace, mun haɗu ne saboda rasuwar abokin mu, Alhaji Sani Dahiru Yakasai. Mun haɗu a wajen jana’iza wacce aka gudanar a fadar sarkin Kano.”
“A na kammala sallah mun tafi maƙabarta a motar sa. Bayan an binne gawar gwamnan ya riƙe hannu na inda yace sai ya ƙarasa abinda ya fara, wato sai ya mayar da ni zuwa gida.”
“Sai na gode masa sannan muka koma tare zuwa gida na. Ba wata siyasa a nan. Kawai mun haɗu ne. Ba mu da wani takun saƙa a tsakanin mu, muna mutunta juna. Kamar Kwankwaso, mu kan haɗu a filin jirgi mu gaisa mu yi raha da juna.”
Zaben Gwamnoni: Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Mika Wata Bukata Ga Al’umma
Wani Sanatan jam’iyyar APC Aliyu Wamakko, ya roki jama’a da su kasance cikin kwanciyar hankali yayin da suka je runfunan zabe domin kada kuri’unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar Asabar.
Wamakko, a wani sako na musamman ga al’ummar jihar Sakkwato, ya ce zaman lafiya shi ne abin da ake bukata na duk wani ci gaba mai ma’ana.