By Ishaq Dabai
An rushe gidan dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya na jihar Bauchi, Yakubu Abdullahi.
Dan majalisar ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ce ta aiwatar da rusau din gidan, wanda ke da nisan mitoci kadan daga gidan shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, a tsohuwar GRA, inda aka rushe shi a daren Juma’a.
Da yake magana a wata hira ta wayar tarho da jaridar Punch a ranar Asabar, Abdullahi ya yi zargin cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya rushe gidansa saboda “dalilan siyasa”.
Yaci gaba da zargin cewa gwamnan yaje wurin kuma yaba da umurnin a rushe gidan wanda kusan kashi 75 cikin dari ya kammala.
“Mun kasance muna jan wannan kusan makonni biyu. A karshe ranar Alhamis, ya aike su cikin dare suka zo da bindigogi suka harbe hudu daga cikin jami’an tsaro na a can.Mun kai rahoton lamarin ga jami’an ‘yan sanda kuma an kai su asibiti inda aka cire harsasan.
“A ranar Juma’a, wannan rukunin yaje gidan da misalin karfe 6 na yamma. Sun zo da bulldozer daga hukumar kare muhalli ta jihar Bauchi, gwamnan yaje wajen da kansa ya umarce su da su rushe gidan, ”in ji Abdullahi.
Lokacin da wakilinmu ya tambaye shi ko yana da hujjojin da za su goyi bayan ikirarinsa na cewa gwamnan yana wurin kuma da gaske yaba da umarnin rushe gidan, Abdullahi yace, “Yaje wurin da kansa.”
Mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, bai amsa tambayoyin da ke neman jin ta bakinsa ba kan batun.
Dan majalisar yace, “Ba wani abu bane dake boye. Ba na nan, amma mutane sun gan shi lokacin daya je wurin. Manyan jami’an gwamnati, ciki har da SSG da kwamishinoninsa, duk suna tare da shi.
Dan majalisan, wanda ya kasance yana fafatawa da gwamnan tun lokacin daya sauya sheka zuwa jam’iyyar a dawa ta APC, yace jami’an gwamnati sun zo sun rubuta a kan shingen gidan, “Hukumar Bunkasa Jiha ta soke shi,” daga baya kuma suka ce suna so su rushe shi.
Comments 1