By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta cafke mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka daban -daban a cikin watanni biyu da suka gabata a fadin jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Wakil, ya fitar ranar Juma’a a Bauchi.
Wakil yace, an cafke wadanda ake zargi da aikata laifuka daban -daban a lokuta da wurare ma ban -banta a fadin jihar.inda ya lissafa laifukan da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, sata, hada baki da kisan kai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rundunar ta kwato bindigar AK-47 guda daya, muggan makamai, kwamfutar tafi-da-gidanka, wayoyin hannu da babur daga hannun wadanda ake zargin.Wakil ya kara da cewa an kama mutanen ne ta hanyar tattara bayanan sirri tare da yin amfani da dabarun ‘yan sanda na gari da dabarun fasaha.
Kazalika Wakil ya kara da cewa, rundunar na kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yayin da yake sake jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin su, wadanda ake zargin, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Comments 1