Bawa Yayiwa Ma’aikatan Jawabi, Tsantseni Da Tarbiyya
Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC, Mista Abdulrasheed Bawa a ranar Litinin, 8 ga Maris, 2021 ya yi jawabi ga ma’aikatan Hukumar a Hedikwatar EFCC da ke Abuja, tare da yin kira ga dukkan ma’aikatan da su kasance masu da’a da sadaukarwa ga ayyukansu.
“Duk Ma’aikata suna da muhimmanci a wannan yaki da cin hanci da rashawa tun daga sama har kasa. Don haka, ina gayyatar kowa da kowa da ya kawo dabaru da kyawawan halaye da za su taimaka wajen tsara wa da sake wa Hukumar fasali don ta zama mafi kyawu duk da nasan ƙalubalen da take fuskanta, “in ji shi.
Bawa ya yi alkawarin ba da fifiko ga walwalar ma’aikata da inganta tsari ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma leken asiri a lokacin aikinsa.
Shugaban na EFCC ya nuna sha’awar yin aiki da manufar bude kofa. Don wannan, ya sanya lambar wayarsa ta sirri ga duk ma’aikatan, yana mai bayyana cewa zai kasance mai karɓar ra’ayoyin da za su kai Hukumar ga wani sabon matsayi.
Haka kuma ya halarci Ofishin shiyya na Abuja da Kwalejin EFCC inda aka yi irin wannan tarurrukan.