Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar ta-baci har zuwa faduwar rana, wanda ta ce da nufin kaucewa tabarbarewar doka da oda, sakamakon tashe-tashen hankula da suka taso a sakamakon tattara sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana hakan ne da safiyar Litinin din nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da dumi-dumi: Kwankwaso Da Buba Galadima Sun Yi Dirar Mikiya A Ofishin INEC
Ya ce an yanke shawarar ne don hana ’yan daba su haifar da hargitsi a cikin halin da ake ciki.
Kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su kasance a cikin gida domin jami’an tsaro ba za su kyale kowa ko kungiyar da ke da niyyar haddasa fitina ba.
Daily Trust ta rawaito cewa, yayin da jami’an tattara sakamakon zabe na kananan hukumomi 44 da jam’iyyar NNPP ke kan gaba da kuri’u sama da 120,000 suka karanto sakamakon zaben, an dage sanar da sakamakon karshe tun karfe 3 na safe saboda batutuwa kan soke wasu rumfunan zaben.
Sai dai jami’in zaben ya kusa fara bayyana sakamakon zaben da karfe 6:48 na safe lokacin da wakilin jam’iyyar APC a cibiyar tattara sakamakon zaben ya fara duba sakamakon zaben.
A wani labarin kuma, INEC Ta Dage Cigaba da Tattara Sakamakon Zaben Jihar Adamawa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jiya lahadi ta dage cigaba da tattara sakamakon zabe a jihar Adamawa har zuwa yau Litinin sakamakon takaddamar sakamakon zaben karamar hukumar Fufore.
Jami’in dake kula da tattara sakamakon zabe na jihar, Farfesa Muhammad Lamin Mele, ya sanar da sakamako daga kananan hukumomi 20 cikin 21 kafin rashin jituwa tsakanin wakilan jam’iyyar kan sahihancin sakamakon na karamar hukumar Fufore.