Wani ma’aikacin jinya a jihar Carlifonia dake Amurka ya kamu da cutar korona fiye da mako guda bayan karɓar rigakafin Pfizer kamar yadda kafar watsa labarai ta Bbc ta labarto.
Wannan lamari ya sa tuni kamfanin da ya samar da rigakafin ya ce “zai yi bitar duk bayanan da ake da su a kan lamari kawo yanzu”.
Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce “Mutane na iya kamuwa da cutar kafin ko bayan rigakafin musamman wanaki 10 na farko bayan yi musu, wanda a wannan lokaci ne rigakafin ke ginuwa a jikin mutum”.
Matthew W., mai shekaru 45, wani ma’aikacin jinya ne da ke aiki a wasu kananan asbitoci biyu, kuma ya fada a wani sakon da ya wallafa a Facebook a ranar 18 ga watan Disamba cewa ya karbi allurar rigakafin ta Pfizer, amma hannunsa ya dan masa ciwo na wuni guda, bayan hakan ba ta da wata illa.