Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Tun bayan da aka daina ganin Umar Sani Jigirya Sallau a cikin shirin Dadin Kowa mutane suke ta cikiyar Ina ya shiga ne?
To sai dai a zantawar sa da Jaridar Dimukaradiyya ya tabbatar da cewa yana nan kuma akwai yiwuwar nan gaba za a ci gaba da ganin sa a cikin shirin na Dadin Kowa.
Sallau yace “Ina nan Kuma Ina ci gaba da harkokina, domin tun kafin na fara shirin Dadin Kowa Ina harkar fim sama da shekaru 20 don haka na koma na ci gaba da harkar fim, Ina shirya fim Mai dogon zango a shafina na Jagora TV a YouTube, sannan Kuma Ina yin harkokin tallace tallace da harkar siyasa, don haka dai duk wata harka dana ke yi bata tsaya ba.”
Daga karshe ya yi Kira ga masu gudanar da shirin fim a matsayin su na jarumai, ya kamata su samar da abin dogaro da Kai ta yadda ko da babu harkar fim din ya zamo kana da abin yi ba Sai ka koma kana yawon maula a wajen wasu ba.
Comments 1