Dattijo ya janye Takarar Gwamna, Hadiza tayi jifa da damar cigaba da zama Mataimakiya, bayan El-Rufa’i ya zaɓi Uba Sani a matsayin magajin shi
Sani Dattijo, tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jahar Kaduna ya sanar da janyewar sa akan ra’ayin sa na tsayawa Takarar Gwamna a Shekarar 2023, biyo bayan amincewa da Gwamnan yayi ma abokin hamayyar sa Uba Sani.
Daily Nigerian ta tattaro cewa, Uba Sani wanda yake Wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya, shine Ɗan Takarar da maƙarraban Gwmanan suka zaɓa, dana kusan Gwamna, da Iyalai da kuma Ƴan Siyasar APC a Jahar.
A wani taron gaggawa na Masu ruwa da tsaki da Gwamna El-Rufa’i ya kirawo a ranar Laraba, Gwamnan ya gabatar da buƙatar zaɓar Ɗan Takara ta hanyar Sasanci, a gaban masu ruwa da tsaki.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Mataimakiyar Gwamnan Jahar Hadiza Sabuwa Balarabe, da Sakataren Gwamnatin Jahar Balarabe Abbas Lawal, Shugaban Majalisar Dokoki Yusuf Zailani, da Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya Uba Sani, tsohon shugaban Ma’aikatar Gwamna, Sani Dattijo da sauran Yardaddun Masu ruwa da tsaki.
Wata Majiyoyi data halarci tattaunawar taron ya naƙalto Gwamnan yana cewa mai gadon shi da Farko itace Mataimakiyar Gwamna Hadiza Balarabe, amma ya jefar da wannan tunanin, bayan ya tattauna da Shuwagabannin Addinai, dana Siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kebbi: Malami Ya Fi Sauran ‘Yan Takara Yin Fice – Matawalle
Gwamnan ya ƙara dacewa, tunda tikitin Hadiza Balarabe bazai iya tafiya a banza ba, to don haka ya zaɓi Mr Sani a matsayin Ɗan Takarar Gwamna daya zaɓa.
Gwamnan ya kuma yi wani canje-canje, inda ya bukaci Hadiza Balarabe ta cigaba a matsayin Abokiyar Takarar Uba Sani, damar da taƙi amincewa da’ita nan take.
Gwamnan ya kuma umarci Mr Dattijo daya canja Mazaɓa, ya nemi Sanatan Kaduna ta Tsakiya.
Waɗanda suka halarci taron sun ce Dattijo nan take yayi gaggawar amincewa da hukuncin Gwamnan cikin farin ciki.
A saƙon daya aike a Dandalin Gangamin yaƙin neman zaben sa, Mr Dattijo yace ya amince da matsayar Gwamnan a matsayin abinda Allah ya ƙaddara, yana mai shan alwashin bada goyon baya ga Ɗan Takarar Sasanci domin samun nasarar shi.
“Salam, ina Son sanar daku, a taron daya wakana a ranar Laraba, Gwamnan ya umarce ni cewa muyi ruwa muyi tsaki, mu nemar wa Uba Sani goyon baya domin ya haye Kujerar Gwamna. Ya kuma umarce ni da in cigaba daga inda Uba Sani ya tsaya a matsayin Sanata mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya,” Saƙon Mr Dattijo.
“A yayinda wannan sakamako bashi muka tsara ba, ko muka so, amma mun amshe shi da ƙaddarawar Allah, wanda yake bada Mulki ga wanda yaso, a lokacin da yaso. A saboda haka, mun miƙa komai a gareshi, tare da addu’a ga Jaha dama Ƙasa data samu nagartattun Shuwagabanni a Shekarar 2023.
“Ina mai cigaba da godiya akan Jagorancin Mallam, da irin goyon bayan shi, wanda nake ɗaukar shi da mahimmanci. Na sayi Tikitin Tsayawa Takarar Gwamnan a APC, Amma zamu sayi na Sanata kamar yanda Allah ya Ƙaddara.
“Ina fatan zamu aiki a tare domin samun nasarar APC a dukkanin zaɓuɓɓukan. Goyon bayan ku, bamu ɗauke shi da wasa ba, kuma zamu cigaba da tunawa da godiya. Allah yabar zumunci.”
A yayinda muƙarraban Gwamnati suka amince da matsayar El-Rufa’i, amma har yanzu, ba’a tabbatar ba cewa sauran Ƴan Takarar da suka haɗa da Manajin-Darakta na Hukumar NIMASA Bashir Jamo, da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Hajji ta Ƙasa NAHCON Abdullahi Mukhtar, zamu amince da hukuncin Gwamnan.