…Tsohon gwamnan jihar Rnugu Sanata Nnamani mai wakiltar mazabar Enugu ta Gabas ya Fice
Sanata Chimaroke Nnamani mai wakiltar mazabar Enugu ta Gabas ya fice daga jam’iyyar PDP.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Nnamani, tsohon gwamnan jihar Enugu wanda ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin, ya bayyana jin dadinsa ga al’ummar mazabar sa bisa goyon bayan da suka ba shi na tsawon shekaru.
A cewar Nnamani, ya tuntubi mukarrabansa da ‘yan mazabarsa kuma ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP saboda rashin jituwar da ba a daidaita tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar na kasa.
KU KARANTA KUMA Tsantsar Raahin Adalci Na PDP Ne Yasa Na Goyi Bayan Tinubu — Nnamani
Ya ci gaba da cewa, ya ci gaba da fatan cewa irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban mazabarsa za ta zama ginshikin ginin da wadanda za su gaje shi za su ci gaba a kai.
Nnamani ya godewa ‘yan Najeriya musamman ‘yan siyasar ‘Ebeano’ ya kuma bukace su da su dage a shekaru masu zuwa.
Tsohon gwamnan ya tabbatar da saninsa da zababben shugaban kasa Sanata Bola Tinubu tare da alkawarin ci gaba da hada kai da shi.
Ya bayyana fatansa cewa gwamnatin da Tinubu ke jagoranta za ta inganta shugabanci nagari, bin doka da oda da kuma kare hakkin dan Adam domin amfanin daukacin ‘yan Najeriya.
Jaridar Solacebace ta ruwaito cewa, Nnamani na daf da tunkarar zaben 2023, ya dage kan cewa ba zai janye shawararsa na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (APC) Tinubu ba, wanda yanzu shi ne zababben shugaban kasa.
A cewar Nnamani, ya yanke shawarar yin jituwa da Tinubu ne, saboda PDP ta karya kundin tsarin mulkinta ta hanyar murguda ka’idar karba-karba.
NAN ta kuma ruwaito cewa Nnamani ya sha kaye a zaben sa na sake tsayawa takarar Sanata a hannun dan takarar jam’iyyar (LP), Kelvin Chukwu.
Dan takarar jam’iyyar LP ya samu kuri’u 69,136 inda ya doke Nnamani na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 48,701. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Bala Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar ranar Asabar.
Gwamna mai ci ya samu kuri’u 525,280 inda ya lashe kujerar.