By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya ba da tabbacin gwamnatinsa na kudiri aniyar aiwatar da aikin hako man da aka riga aka gano a yankin Kolmani na masarautar Pindiga ta jihar Gombe.
Yahaya ya bayyana haka ne a ranar Asabar din da ta gabata, yayin wani liyafa da aka shirya domin karrama Mukaddashin babban Alkalin Jihar, Mai Shari’a Muazu Pindiga mai ritaya, a garin Pindiga da ke karamar hukumar Akko.
A cewar gwamnan, kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ta hannun sashin binciken da ake kira Frontier Exploration na hukumar ya zuba dimbin albarkatu, kuma an gano wani adadi mai yawa na man da za a iya kasuwanci da shi, wanda ya kai sama da ganga biliyan 6 a yankin Kolmani.
Ya ce a lokuta da dama ya ziyarci hedikwatar kamfanin na NNPC sannan kuma ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa da su kan yadda jihar za ta iya cin gajiyar arzikin man fetur da iskar gas a jihar.
Sannan ya ce, “Amma saboda tabarbarewar tattalin arziki da aka fuskanta a baya-bayan nan, wanda Covid-19 ya yi wa katutu, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen fara aikin hako danyen mai sama da biliyan 6 a yankin; amma ina mai tabbatar muku da hakan zai faru, kuma na kuduri aniyar ganin hakan.”
Yahaya ya bukaci tsohon mai shari’a na jihar Gombe, Mai shari’a Pindiga, da kada ya yi watsi da tarar sa da suka nuna masa a matsayin alkali na gaskiya a gidan shari’a.
Gwamnan ya bayyana fatansa na cewa murabus din mai shari’a Muazu Pindiga zai kara ba shi dama don ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar yankinsa na Pindiga da jihar da kasa baki daya.
Sannan ya yabawa al’ummar Masarautar Pindiga bisa jajircewar da suka nuna wajen goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa, inda ya yi musu alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta mayar da martani ta hanyar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da ke da kimar zamantakewa da tattalin arziki ga jama’a.
Shugaban taron kuma tsohon Ministan Sufuri, Sanata Abdullahi Umar ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya gudunmawa musamman yadda ake gudanar da cikakken aikin hako mai a Kolmani na Masarautar Pindiga.
Ya kuma mika godiyarsa ga mai martaba Sarkin Pindiga da ya ga ya dace a karrama mai shari’a Muazu Pindiga mai ritaya, inda ya yi nuni da cewa dimbin jama’ar da suka zo wurin taron liyafar suna nuni da cewa limamin shari’a mai ritaya mutun ne na al’umma.
A sakon ta na fatan alheri, tsohuwar shugabar kotun daukaka kara, Mai shari’a Zainab Bulkachuwa, ta bayyana gamsuwarta da yadda gwamnan ya gudanar da ayyukansa cikin kankanin lokaci da ya hau karagar mulki.
Bulkachuwa ta kuma taya mai shari’a Muazu Pindiga mai ritaya murnar samun nasarar ficewa daga aikin shari’a ba tare da aibu ba, ya kuma godewa Masarautar Pindiga bisa karramawar da aka yi masa.
Mai martaba Sarkin Pindiga, Muhammad Ahmed, a nasa jawabin, ya bayyana cewa rikicin da ake yi tsakanin jihohin Gombe da Bauchi kan rijiyar mai na Kolmani ba zai haifar da wata baraka a tsakanin jihohin biyu ba.