Wani mazaunin wani kauye da ke kasar Uganda ya ce matansa 12 wadanda dakyar yake tuna sunayensu, da yara 102 tare da jikoki 578 sun ishe shi, Daily mail ta ruwaito.
Kamar wasa, yanzu sun zame masa matsala, yanzu haka ba ya da aiki, ya sanar da manema labarai a cikin gidansa da ke kauyen Bugisa a yankin Butaleja a gabashin Uganda.
KU KARANTA: Mahaifina ya fatattaki mahaifiyata saboda tana haihuwa yara mata ga shi yanzu mu ke ciyar da gidan
Ya bayyana cewa:
“Yanzu da ba ni da isasshiyar lafiya kuma gidana ya fara mana kunci, matana 2 sun tsere saboda ba na iya daukar dawainiyar abubuwa kamar abinci, ilimi da suttura.”
Hasahya, wanda mutane ke yawan zuwa ganinsa a kauyen ya ce matansa yanzu suna shan magungunan tsayar da haihuwa.
Kuma ba ya da ran za su kara haihuwa saboda ya koyi hankali bayan tara iyalan da ba ya iya kulawa da su.
Ya auri matarsa ta farko a 1972 a wani shagalin gargajiya yayin da suke da shekaru 17 da haihuwa kuma diyarsa ta farko, Sandra Nabwire suka fara haihuwa a shekarar.
Ya ce saboda su biyu kadai aka haifa, dan uwansa da jama’a ne suka ba shi shawarar yin aure-aure don yawaita iyalai.
A baya yana siyar da shanu ne tare da fawa. Kuma yana ta ba da auren yaransa mata kasa da shekaru 18.
Yanzu yaran Hasahya guda 102, shekarunsu tsakanin 10 ne zuwa 50, kuma amaryarsa yanzu shekarunta 35.
Saidai ba ya iya tuna sunayensu gabadaya sai ya dauko wani tsohon littafin da ya rubuta sunayensu.
Allah Mai Iko: Bayan Kwashe Shekara 20 Tana Jiran Haihuwa, Wata Matar Aure Ta Haifi Tagwaye
Wata matar aure ƴar Najeriya na cike da matuƙar farin ciki na samun tagwaye bayan ta kwashe shekara ashirin tana jiran samun haihuwa.
Matar auren yanzu haka na cike da tsananin farin ciki bisa wannan abin arziƙin da ya samu ahalin ta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
An sanya hotunan matar da na tagwayen ta a Facebook inda mutane da dama suka yi ta taya ta murna.
Tuni mutane da dama suka fara taya matar murna inda suma garzaya wajen yin sharhi domin yin fatan alkhairi ga jariran.