Hukumar gudanarwar Jami’ar Obafemi Awolowo dake garin Ile-Ife, a ranar Talata, ta bayyana ranar da za a ci gaba da gudanar da harkokin karantun ta. Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito
Hukumar gudanarwar ta dai sanya ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoban shekarar 2022 a matsayin rarar komawa makarantar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga Sun Kashe Mai Unguwa, Da Wasu Mutum 2 Tare Da Garkuwa Da Wasu Da Dama
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun magatakarda kuma sakataren majalisar zartaswar jami’ar da ya rabawa manema labarai a Osogbo, hukumar jami’ar ta OAU ta umurci dalibanta da su koma makaranta daga gobe Laraba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Daliban Jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife, an umurci daliban da su koma dakunan kwanansu dake cikin makarantar a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba shekarar 2022, yayin da za a fara gudanar da cikakken ayyukan karatun ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba shekarar 2022 don ci gaban zangon karatun shekarar 2021 da 2022.
“An yanke shawarar hakan ne a wani taro na musamman na Majalisar Dattawan Jami’ar, wanda aka gudanar a dakin taro na Oduduwa a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba, 2022.
“A madadin mahukunta da Majalisar Dattawa ta Jami’ar, muna yi wa dalibanmu fatan cigaba da zangon karatu ba tare da katsewa ba da kuma tafiya lafiya daga wuraren da suke zuwa makarantar”
A WANI LABARIN KUMA: An Kama Mutane 80 Da Ake zargi Da Taimakawa Yan bindiga – Gwamnatin Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane 80 bisa laifin taimakawa ‘yan bindiga. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An dai tsare su ne bisa zarginsu da hannu wajen aikata fashi da makami da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.