Wata mata a unguwar Marapodi, cikin birnin Lusaka a ƙasar Zambia, ta sume a kotun Matero, bayan mijinta ya ƙi yarda su cigaba da aure inda yace addinin sa ya hana shi auren mata biyu.
A cewar rahoton Tribune, sai mutane suka yi da gaske sannan suka farfaɗo da Jane Zulu, mai shekara 33, wacce ta sume jim kaɗan bayan ta fita daga harabar kotun wacce majistare Gaston Kalala ke jagoranta.
KU KARANTA KUMA: Zaben Gwamna: INEC Ta Tabbatar Da Halastaccen Dan takarar Jam’iyyar PDP A Ogun
Jane ta kai Gilbert Zulu, mai shekara 42, kotu ne da fatan cewa za a sanya shi ya ɗauki auren su na shekara huɗu da muhimmanci.
Buƙatun da take nema a gaban kotun sun haɗa da dole a sanya Gilbert musu kwana ita da kishiyar ta, sannan kuma ya bayyana a gaban ƴan’uwan sa, kotu da matar sa ta farko cewa ita ma halastacciyar matar sa ce.
Tayi ƙorafi ga kotun cewa duk da ya biya sadakin ta a shekarar 2018, sannan ya ɗaga darajar ta daga saɗaka zuwa matar sa, Gilbert kwana ɗaya kawai yake yi a sati a ɗakin ta yayin da yake sauran kwanakin a wajen ɗayar matar sa.
Jane tayi bayanin cewa duk da cewa ta sha kiran taron ƴan’uwan s domin ya gaya musu cewa ita matar sa ce, ya ƙi yayi hakan.
Alƙalin kotun dai ya ƙi sasanta tsakanin su, inda yace Gilbert wasa da hankali kawai yake mata sannan ya buƙace su da su nemi a raba auren.
Bayan Sun Rabu Da Budurwarsa, Matashi Ya Koma Roƙon Su Cigaba Da Soyayya, Hirar Su Ta Bayyana
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koma magiya a wajen budurwar da suka rabu kan ta amince su cigaba da soyayya.
Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Darasimi Oyewole ta wallafa hirar da suka yi a WhatsApp da tsohon saurayin ta mai suna Simeon, wanda yake son su dawo su cigaba da soyayya.
Darasimi ta bayyana cewa ya ci mutuncin ta wanda ya kai har sai da ya zazzagi mahaifiyar ta lokacin da ya ƙi sauraron ta.