Na tarkata gabadaya kudadena na kai budurwata Dubai, bayan dawowarmu ta fara korafi kan ba ni da maiƙo yanzu, in ji wani matashi, YEN.com.gh ta ruwaito.
Matashin ya bayyana yadda budurwarsa ta yi masa butulci bayan ya tattara gabadaya kudadensa ya kai ta kasar Dubai.
KU KARANTA: Matashi ya kai ƙarar budurwarsa yana neman N7.5b kan ƙin amincewa da soyayyarsa
Ya bayyana cewa:
“Na kai budurwata hutu a watan da ya gabata kasancewar tana yawan korafi kan yadda kawayenta ke yawan fita yawon bude ido amma ban taba kai ta ba.
“Na kai ta Dubai da duk kudaden da na dade ina tarawa na fiye da shekara daya. Tana aiki amma bata saka ko sisi ba, ko kudin abinci balle tikiti bata biya ba.
“Ni na biya kudin masauki, kayan sawanta, shakatawa, abinci, kayan sha, kitso, kumba da sauransu ba tare da korafi ba.
“Na ji dadi kan yadda ta yi farincikin fita yawon na makonni biyu. Mun dawo kuma yanzu haka tana wurina saboda na yi amfani da kudina don biyan kudin yawon.
“Yanzu tana yunkurin rabuwa da ni saboda ban samar mata da komai. Ta ce akalla a matsayina na namiji ya dace in dinga siya mata komai. Amma shin wannan adalci ne? Shin wanda ke son ka zai sanya ka yin hakan?”
Ya nemi jin shawarar jama’a kan wannan budurwar tasa.
Naga Ta Kaina: Wata Budurwa Ta Koka Kan Irin Kuɗin Da Banki Suka Lafketa Da Su
Cike da takaici wata budurwa ƴar Najeriya mai rayuwa a birnin Jos, jihar Filato, ta bayyana abinda ya faru da ita bayan taje banki.
A cewar budurwar, taje bankin kasuwanci na First Bank domin ciro kuɗi inda aka bata ƴan ₦50 a kanta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Abin takaici bayan ta koma gida, sai ta duba kuɗin taga duk sun lallace sun koma yagaggu.
Ta roƙi ƴan Najeriya da su kawo mata ɗauki, inda ta ƙara da cewa ba wani mai kasuwancin da zai karɓi waɗannan kuɗin a hannun ta.