Dama muna kallon macizai a matsayin mugayen dabbobi kuma muna guje musu, yayin da wasu da suka fuskanci cizon suke kulawa da su tare da dakatar da su daga cizon wasu.
Saidai ba kowa bane yake yin hakan, weloveanimals ta ruwaito. Ba a dade ba wani mazaunin Indiya ya fuskanci cizon maciji daga nan ya kama shi ya cije shi har sai da yaga macijin ba ya motsi.
KU KARANTA: Yadda ambaliyar ruwa ta janyo ƙaruwar macizai a arewa, matar dagaci ta rasu
Mutumin mai suna Kishore Badra yanzu haka yana zama ne a kauyen Ganbhatipatisa, wani yanki na kauyen Odishi da ke kasar Indiya.
Yayin da Badra ke hanyar dawowa gida daga wurin aiki ne macijin ya cije shi a kafa. Bayan ya ji bakar azaba and a kama dabban ya dinga gartsa masa cizo har sai da yaga ya mutu.
Badra ya ce laminny faru ne bayan jin azabar cizo, hakan yasa ya haska tocila inda yaga maciji mai suffar kunama.
Sakamakon hakan, bai yi wani tunani ba ya cije shi har sai da ya ga ya mutu. Ya dauki gawar macijin inda ya kai gidansa don ya nuna wa matarsa.
Anan ne matar da sauran mazauna kauyen suka sha mamaki inda suka nemi ya ke asibiti don a duba shi. Saidai Badra bai je ba saboda ya kasa.
Ya nufi wurin mai ba da maganin dafin maciji don a ba shi magani. Bayan saka labarin a kafafen sada zumuntar zamani na Indiya, nan da nan abu ya yadu.
Mutane da dama sun musanta labarin inda masana suka dinga mamakin yadda ya rayu bayan irin wannan nau’in macijin ya cije shi kuma ya rayu.
Kuma matsawar hakan ne ya faru, to tabbas Badra mutum ne mai sa’a a rayuwarsa.
Wata Mata ta Sanya Shirgegen Maciji a Gawar Mijinta aka bisne su tare
An hasko wata mata yar kassr Ghana a wani Faifan bidiyo tana sanya maciji da ran shi cikin gawar mijin ta gabannin a bisne shi.
Bidiyon wanda ya yi ta karade shafukan sada zumunta na zamani, ya nuna yadda matar ta rataye shirgegen macijin a wuyar ta kafin daga bisani ta cire ta jefar cikin akwatin gawar.
Sai dai gabannin cire macijin an ji yadda take wata magana ta surkulle da mijin nata, inda aka gaza gane abin da take nufi.