Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yanzu haka ‘yan Najeriya sun koma suna cin shinkafar gida da aka noma bayan rufe kan iyakokin kasar.
Buhari ya yabawa manoman kasar kan yadda suke noman shinkafa da sauran kayan abinci.
Shugaban ya bayyana jin dadinsa da yadda manufofinsa na noma na gwamnati ke aiki yadda ya kamata.
Ya yi wannan jawabi ne a Katsina ranar Juma’a a wani taro da zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar.
Buhari ya ce yana da kyakkyawar fahimtar Najeriya da al’ummarta, don haka ake samar da tsare-tsare na noma.
“Na ce dole ne mu noma abin da muke ci, mu ci abin da muka noma, wannan kasa ce da ta taba dogaro da shinkafar kasar waje.
“Mun rufe iyaka da shinkafar waje, na ce me ya sa ba za mu iya cin shinkafar Najeriya ba, kuma da tsarin da aka yi, ‘yan Najeriya suna cin shinkafar gida.”
Buhari ya lura cewa aiwatar da asusun bai daya na Treasury Single Account (TSA) ya taimaka wa gwamnati wajen dakile jami’an gwamnati marasa kishin kasa.
“Na sami wani mutum mai tauri (Hamid Ali) don aikin Kwastam. Ya zo wurina ya ce sun damke tankunan mai guda 20 da suke shirin tsallakawa kan iyaka.
“Na ce masa, “ka sayar da man da tankunan man ka sanya kudin a cikin asusun TSA”. Ya kara da cewa kudin da za su sami hanyar zuwa ga asusun gwamnati masu yawa.