Sabuwar shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta bayyana kudurinta na sauya salon yaki da korona. Inda ta ce za ta kaddamar da gagaruman sauyin da kasar za ta yi kan cutar korona.
Samia Suluhu Hassan ta bayyana hakan ne a wurin rantsar da ministocin gwamnatinta a ranar Talata, ta kuma sanar da rantsar da runduna ta musamman da za ta dinga bai wa gwamnati shawara kan matakan da ya kamata a dauka na shawo kan annobar cutar korona.
Wannan ya sha bamban da abin da tsohon shugaban kasar marigayi John Magufuli ya dauka, inda ya sha yin watsi da bullar cutar korona a Tanzania.