Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane da dama a kauyen Garawa, karamar hukumar Giwa jihar Kaduna.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da rundunar sojin sama ta samu nasarar kakkabe wasu ‘yan bindiga a garuruwan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.
Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Mr Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Aruwan ya bayyana cewa hukumar tsaro na ci gaba da bincike kan harin da aka kai Giwa, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a yankin.
Ya ce yan bindigar sun kai hari tare da kashe mutane biyu a wurare daban daban da ke a karamar hukumar.
A cewar sa, an kashe Alhaji Sa’adu a gundumar Fatika yayin da yan bindigar suka sace wasu mutane.