Bayan Osun, Villa ita ce inda PDP zata je — Inji Ayu
Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa Dr Iyorchia Ayu, a ranar Lahadi yace nasarar Ademola Adeleke a zaɓen Gwamnan Jahar Osun wata alama ce ta abinda za’a gani a babban zaɓen 2023.
Da yake maida jawabi akan sakamakon zaben a ranar Lahadi, Ayu a cikin sanarwar daya fitar yace “zaɓen ya nuna an gaji da Jam’iyyar APC, kuma ya nuna ƴan Najeriya suna so PDP ta dawo da mulki, kuma PDP na nan zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Agaji Ta Saudiyya Za Ta Kafa Jami’a A Zamfara
Shugaban yace shekaru sha biyu da suka gabata “PDP ta rasa Jahar Osun, ba ta hanyar zaɓe ba, amma ta hanyar ƙwace wa daga Jam’iyya mai mulki.
“shekaru hudu da suka gabata, PDP ta lashe zaɓen Gwamna, amma an sace Mata nasarar ta. Mun dawo kuma mun amshe mulkin da aka ƙwace mana”.
Shugaban Jam’iyyar Hamayyar ya yabawa Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta INEC da Jami’an tsaro kan tabbatar da cewa ƙuri’un da aka kada an ƙirga su.
“Muna kira ga ƴan PDP da ƴan Najeriya dasu bi turbar PDP. Kada a bar su baya, domin faɗawa Villa.
“Da Jam’iyyar PDP, ƴan Najeriya, zasu sake cigaba . Tuni Al’ummar Osun sun yi magana. Wanda ya rage sauran ƴan Najeriya suma suyi magana a 25 ga watan Fabrairu na Shekarar 2023.
Sanarwar ta godewa Al’ummar Osun da basu yarda an yi amfani dasu ba, an saye su da abinci da kudi.kunce bazaku sayar da ƙuri’ar ku ba.