Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Darasimi Oyewole ta wallafa hirar da suka yi a WhatsApp da tsohon saurayin ta mai suna Simeon, wanda yake son su dawo su cigaba da soyayya.
Darasimi ta bayyana cewa ya ci mutuncin ta wanda ya kai har sai da ya zazzagi mahaifiyar ta lokacin da ya ƙi sauraron ta. Jaridar Legit.ng ta rahoto
KU KARANTA KUMA: An kai wani mummunan hari bam a Afghanistan, mutane da dama sun jikkata
Watanni shida bayan aukuwar hakan, sai ya dawo yana neman su sasanta, inda ya bayyana cewa rayuwar sa ta shiga garari tun bayan da suka rabu.
A cewar Simeon, yayi ta yin addu’a da azumi inda daga ƙarshe ubangiji ya nuna masa cewa yana buƙatar ta a rayuwar sa domin ya cimma ƙaddarar sa.
“Eh tabbas nasan ban kyauta miki ba kuma a shirye nake na gyara kura-kurai na.”
“Tun lokacin da muka rabu, rayuwata ta shiga garari ta sauya gabaɗaya, Ubangiji ya sha nuna min ke. Nayi addu’o’i da azumi.
“Ina buƙatar ki a rayuwa ta.” Ya gaya mata.
Darasimi ta caccake shi kan yadda ya ƙi sauraron ta a baya sannan daga baya ta gaya masa cewa ita yanzu matar aure ce, amma dai ta yarda za su iya yin abota.
Ga bidiyon hirar su a nan
“Ban Damu Da Auren Wanda Bana So Ba Indai Har Yana Kuɗi” Jarumar Fim
A wani labarin na daban kuma, wata jarumar fim ta bayyana muhimmancin kuɗi a soyayya.
Jarumar finafinan masana’antar Nollywood, Charity Nnaji, tayi magana akan muhimmancin kuɗi a cikin soyayya ko aure.
A wata tattaunawa da tayi da majiyar mu, jarumar finafinan ta bayyana cewa kuɗi suna daga cikin muhimman abubuwan da take lura da su yayin zaɓar wands zata yi soyayya da shi.