By Abbas Yakubu Yaura
Daya daga cikin ‘yan takarar sanata da suka fafata a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar kwanan nan a mazabar Oyo ta tsakiya, Injiniya Faozy Oladotun Nurudeen, ya fice daga jam’iyyar.
Nurudeen, ya ce ya fice daga APC ya koma jam’iyyar Accord.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: INEC Ta Ki Amincewa Da Lawan, Tace Machina Ne Ya Lashe Tikitin Takarar APC A Yobe Ta Arewa
Faozy Nurudeen Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Nurudeen na daya daga cikin ‘yan takara bakwai da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar Sanatan Oyo ta tsakiya a jam’iyyar APC.
Dan siyasar a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a ya bayyana cewa zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ba wakilci ne na zabin jama’a da gaske ba.
Ya kara da cewa ya shiga jam’iyyar Accord Party ne domin ceto al’ummar yankin mazabar sa a majalisar dattawa.
Ya kuma bayyana cewa ya yi niyyar cimma burinsa a jam’iyyar APC, amma zaben fidda gwani ba na dimokuradiyya ba ne.
Sannan ya ce ya fice daga APC zuwa Accord Party ne sakamakon rashin bin tsarin dimokaradiyyar APC.
Ya kara da cewa, “Wannan shi ne don sanar da kowa da kowa game da ficewata daga jam’iyyar APC. Dole ne wakilci na gaskiya ya nuna ainihin dimokuradiyya.
“Lokacin da muka fara wannan tafiya, lallai ne domin mu kawo wa mutanen yankin Oyo ta tsakiya wakilci nagari, hakan ne muka yi niyyar cimmawa a karkashin jam’iyyar APC.
“Duk da haka, zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC ba su wakilci ainihin zabin mutane ba. Wannan ba zai hana mu ba, wannan ba zai hana mu ba.
“Kudirinmu mai sauki ne. Yunkurin isar da kyakkyawan shugabanci ga jama’a ne ya sa mu ba tare da la’akari da jam’iyya ko tsarin siyasa ba, don haka yanzu mun zabi jam’iyyar Accord Party don gudanar da wannan aiki”.