By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an saki wani firist na cocin Katolika, Rev. Father Mark Chimezie Godfrey, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 13 ga watan Oktoba,2021 a Umuahia, kuma ya kubuta a ranar 23 ga watan Oktoba, 2021, bayan ya shafe kwanaki goma tare da wadanda suka sace shi.
Diocese na Katolika na Umuahia ta sanar da sakin limamin ta, ta cikin wata sanarwa da Bishop na Umuahia, Lucius Iwejuru Ugorji ya sanya wa hannu. Bishop din ya cigaba da godewa Allah daya amsa addu’ar diocese din.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rev Fr Mark Chimezie Godfrey na St Theresa’s Parish Umuahia wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace shi a hanyar Enyiukwu, Afaraukwu Ibeku a ranar 13 ga oktoba a karamar hukumar Umuahia ta Arewa ta jihar Abia.
Bishop Ugorji ya kuma nuna matukar godiyarsa ga dukkan bishop -bishop, firistoci, maza da mata da aka tsarkake da kuma duk masu aminci Kiristoci wadanda suka taimaka cikin addu’o’i a cikin mawuyacin lokaci da kokarin da firist ke cikin bauta dan samun kubuta.
Sai dai sakin nasa bai bayyana cewa ko an biya kudin fansa ba, ko ba’a biyaba