Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya amince da fara aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga kwararrun malamai 4,491 a karkashin tsarin albashin ma’aikatan kananan hukumomin jihar daga ranar 1 ga watan Agusta, 2022.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Zulum ta fuskanci tuhuma a kafafen sada zumunta a makon da ya gabata cewa malaman da ke aiki da makarantun firamare na karbar albashi a wata-wata tsakanin Naira 7,000 zuwa Naira 11,000 a matsayin albashin su.
Gwamna Babagana Zulum wanda ya dawo daga kasar Japan bayan wata ganawa da ya yi a hukumance ya amince lokacin da yake ganawa da shuwagabannin hukumar da ma’aikatan gwamnati da na kananan hukumomi da shugaban ma’aikata da kuma mambobin kungiyar malamai ta Najeriya NUT. da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a gidan gwamnati dake Maiduguri ranar Laraba.
Ƙungiyar Ƴan Jarida NUJ ta yi Allah-wadai da taɓa Mambanta, tace zata ɗauki mummunan Mataki
Zulum ya kuma bayar da tabbacin cewa za a fara aiwatar da ci gaban karin girma ga daukacin ma’aikatan jihar daga watan Janairun 2022 zuwa 2023 bayan an gudanar da jarrabawar karin girma, yana mai jaddada cewa idan jihar Yobe za ta iya yin jarrabawar karin girman, me zai hana Borno yin hakan.
” Matsalolin da ke faruwa a ma’aikatan gwamnati da na kananan hukumomi suna da yawa. Mutane da yawa sun kasa fahimtar matsalolin da muke fukanta, amma ina tabbatar muku za mu zauna mu magance su cikin lokaci,” in ji shi.
Ya koka da cewa kimanin malamai 3,000 da ke karban albashin a jihar ba su da wata kwakkwarar takaddar shedar fanni koyarwa, amma ya ba da tabbacin cewa za a horar da wadanda suka cancanta.
“Za mu dauki malamai 1000 da za a basu horo su a kwalejojin ilimi Biu da Bama, yayin da za a horar da wasu tare da hadin gwiwar cibiyoyin malamai na kasa (NTI) na tsawon watanni 6, idan suka ci jarrabawar za a sa su cikin tsarin”, ya kara jaddada.
Tun da farko, Shugaban kungiyar NLC na jihar Borno, Kwamared Yusuf Inuwa ya yabawa Gwamna Zulum bisa biyan hakkokin ma’aikatan na shekarar 2020, tare da ba shi tabbacin cewa kungiyar na ci gaba da bai wa gwamnatinsa hadin kai da goyon bayan masana’antu.