Wani tsohon ‘dan wasan baya na kungiyar kwallon kafar ta kasar Faransa Jean-Pierre Adams ya rasu ya na da shekaru 73 a duniya bayan ya kwashe shekara 39 a sume.
Adams wanda ya yi wa Faransa wasa a matakin kasa har sau 22 a shekarun 1970 ya suma ne sakamakon wani kuskuren allurar da aka masa a shekarar 1982 lokacin da ake masa aiki a guiwarsa.
A lokacin rayuwarsa ya buga kwallo a kungiyar Faransa ta Marius Tresor da ’the black guard’.
Kungiyar Nimes da ya yiwa wasa ta aike da sakon ta’aziya da ‘yan uwa da iyalan Adams bisa rasuwarsa.
Lokacin ganiyar wasan sa, Adams ya yiwa kungiyoyin Nice da PSG wasa a gasar wasannin kasar.
An haifi Adams a shekarar 1948 a Dakar dake kasar Senegal, kuma yana daya daga cikin ‘yan wasa na farko da aka haifa a wajen Faransa da ya yiwa kasar wasa.