Bayan shekaru 3 da tsige shi, Sarki Sanusi Ya ziyarci Kano
Kimanin shekaru uku da tsige shi a matsayin Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya kawo ziyara jihar a ranar Laraba.
Gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta tsige Sanusi ne a ranar 9 ga Maris, 2020 bisa zargin rashin biyayya.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC ta buƙaci Ƴan Sanda dasu daina gayyatar Fani-Kayode kan kalamansa
Da farko an kai shi zuwa kauyen Loko da ke jihar Nassarawa inda daga baya aka kai shi garin Awe.
An tsare tsohon Sarkin ne a garin Awe har zuwa ranar 13 ga Maris, 2020, inda kotu ta ce a ba shi ‘yanci.
Da ya isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano, Malam Sanusi wanda shi ne Jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya ya wuce gidan mahaifiyarsa da ke kan titin Ibrahim Dabo a cikin birnin Kano.
A wani faifan bidiyo, an ga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, sanye da kayan sarki, yana musabaha da tawaga da ‘yan uwa da masu rike da mukaman gargajiya da kuma masu hannu da shuni.
Wata majiya da ke kusa da Sarkin ta bayyana cewa, Sanusi na Kano a kan hanyarsa ta zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa, amma ya tsaya a Kano saboda rashin kyawun yanayi.
“Sarkin ba zai iya zuwa jihar Jigawa kai tsaye ba saboda rashin kyawun yanayi, kuma a lokacin da ya isa Kano, magoya bayansa da suka samu labarin zuwansa suka mamaye filin jirgin domin ganinsa.
“Bayan haka, ya yanke shawarar je ya gaida mahaifiyarsa,” in ji majiyar.
Sai dai majiyar ta ce a matsayinsa na dan kasa tsohon sarkin yana da damar zuwa duk inda ya ga dama, yana mai jaddada cewa har kotu ta yanke masa hukuncin zuwa duk jihar da yake so a kasar.
A wani labarin kuma: EFCC tace za ta hana sayen kuri’u a Najeriya – Bawa
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar wa ‘yan Najeriya a shirye da kuma iyawarta na magance sayen kuri’u da sauran ayyukan magudin zabe domin tabbatar da zaben 2023 cikin gaskiya da adalci.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba, ya ruwaito shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, yana fadar haka a taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa ta tsakiya kan babban zaben 2023.