Tauraron dan wasan kwallon kafar Faransa Tiemoue Bakayoko na shirin barin Chelsea bayan ya shafe shekaru biyar a kungiyar.
Dan wasan ya amince da yarjejeniya da Marseille ta Faransa a wannan bazara.
Dan wasan mai shekaru 27 ya kasance babban dan wasan Chelsea a shekarar 2017 lokacin da ya koma kuniyar daga Monaco kan fan miliyan 40.
Sai dai zamansa a Stamford Bridge bai tafi kamar yadda ake tsammani ba domin al’amuran wasanni ba su daidaita ba ga dan wasan na Faransa.
Bafaranshen ya buga wa Blues wasanni 43 a dukkannin gasanni, inda ya zura kwallaye uku tare da lashe kofin FA.
Al’amura sun tabarbare a kulob din kuma bai buga wa Chelsea wasa ba tun kakar 2017/18, maimakon haka ya bar kulob din a matsayin aro.
Ya buga wasan aro a AC Milan, Monaco, Napoli, sannan kuma a AC Milan, inda ya lashe kofin Seria A a wasan karshe.
Jaridar Foot Mercato ta Faransa ta ruwaito cewa a yanzu akwai yuwuwar ya fice daga kungiyar ta Chelsea dake yammacin London a yarjejeniyar dindindin
Ya kuma amince da yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Marseille dake Faransa.
A wnai labarin kuma na daban.
Ƴan bindiga sun sace mai Juna biyu a Kaduna
Ƴan bindiga sun sace mai ciki a Al’ummar Lema, Mando kusa da Makarantar Horasda Manyan Sojoji ta Zaria, Jahar Kaduna.
Sun sace wasu mutane bakwai a lokacin da ƴan bindiga suka shiga gidaje da misalin ƙarfe 1 na safe a ranar Lahadi.
Wani daga cikin mazauna yankin, Musa Danladi ya bayyana cewar duk sunji tsoron su fito daga gidan su, saboda harbin bindiga.
“Sun zo ne da misalin ƙarfe 1 na dare, sun tafi da mutane 8 ciki har da mace mai juna biyu a garin. Wannan ba shine lokaci na farko da ƴan bindiga suka kawo hari a ƙauyen”, Inji shi.
Wasu mazauna garin sun yi kira ga Gwamnatin Jahar data kawo masu ɗauki.
Har yanzu Gwamnati bata ce komai ba akan lamarin, amma Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Mohammed Jalige yace zai bincika ya gano lamarin tare da sanar da abinda ya faru.
Kuma bai fadi komai ba game da lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.