Mahukunta a Kasar Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo sun bayyana cewa cutar Ebola da ta sake barkewa a kasar tare da sanadiyyar salwantar rayukan mutane shida ta yi bankwana da kasar.
Wannan sanarwabta Mahukunta ta zo ne watanni uku bayan sake bullar cutar a yankin Kivu dake gabashin kasar.
Cikin wata sanarwa da ta fitat, hukumar dake kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta ce matakin kakkabe cutar ya biyo bayan namijin kokari ne da mahukunta tare da masu bada agaji na duniya suka yi.
Wannan shine kari na uku da cutar ke ballewa cikin kasa da shekara guda kachal a kasar.
Gabannin sake bullar cutar a watan Faburairu, kasar ta sanar da kawo karshen ta karo na sha ɗaya, wacce ta yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane 55 cikin 130 da suka kamu cikin watanni bakwai.
A na yan baya-bayan nan mutane 11 ne auka kamu yayin da shida daga ciki suka riga mu gidan gaskiya.