Majalissar Dokokin kasar Fakistan za ta zabi sabon Faraministan a yau Litinin bayan ta hammarar da gwamnatin Imran Khan ta hanyar kada kuri’ar yankan kauna da sanyin safiyar jiya Lahadi.
Ana dai gyautata zaton cewa jagoran Yan adawar kasar Shahbaz Sharif ne zai maye gurbin Mr Khan ta hanyar samun kuri’u mafi rinjaye a zaben.
Majalissar dai zata fara kada kuri’a ne da mulisamlin karfe biyu na rana agogon kasar, dai dai da karfe 9 na safe agogon GMT.
An dai tumbuke Mr Khan Mai shekaru 69 daga garagarshi ne bayan wani takaddamar siyasa da ya barke tsakaninsa da Yan Majalissar kasar, da kuma shiga tsakanin da wata Kotun Kolin kasar ta yi.
A baya dai yayi kokarin kaucewa wannan mataki na majalissar Dokokin kasar ta hanyar ruguzasu da kuma yin shelar gudanar da zaben gaggawa domin dakile kudurin na hammarar da Kujerarsa, lamarin da ya citira, bayan hukuncin Kotun.
BBC/ULR