Jami’an rundunar yan sanda daga sashi daban-daban sun yi dafifi a kafatanin hanyoyin dake Isa zuwa harabar Majalissar Dokokin jihar Cross Rivers.
Shaidun gani da Ido sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, yan sandan sun yi taron farin dango ne a yankin, tun da misalin karfe 6 na sanyin safiyar yau Talata.
Kana rahotanni sun bayyana cewa, an hango jami’an Yan sandan a cikin Zauren majalissar Dokokin jihar na Cross Rivers, yayin da kuma wasu jami’an suka yi cin-ci-rindo a kusa da Ofishin Gwamna Ben Ayade.
Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan Wata babbar Kotun dake zamanta a Abuja, ta yanke hukuncin korar wasu Majalissun jihar 20 daga mukamin su, biyo bayan sauya sheka zuwa jam’iyar APC da suka yi, lamarin da Jam’iyyar mai mulki ta yi ikirarin cewa ta shigar da kara kotun daukaka kara domin a dakatar da aiwatar da hukuncin na Kotun tarayya.
A wani labarin Kuma na daban.
PDP a Cross River na Murna akan Korar Ƴan Majalisu 20 — Cewar Ikem
Jam’iyyar PDP ta yabawa Babbar Kotu data kori ƴan Majalisu 20 da suka canja Jam’iyyar zuwa wata a ƴan kwanakin da suka gabata.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Jahar Mr Venatius Ikem a ranar Talata yace Mambobin Jam’iyyar na matuƙar jindaɗi akan hukuncin daya kori ƴan majalisun da suka koma Jam’iyyar APC.
A yanke hukuncin da Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya yanke a ranar 21 ga watan Maris, Kotun tace akwai buƙatar subar kujerun su, tunda suka ƙyale Jam’iyyar data yi sanadin kawo su a kujerar.
Hukuncin ya biyo bayan wata ƙara da Jam’iyyar PDP ta shigar mai Lamba ta FHC/ABJ/CS/975/2021.
Shugaban Jam’iyyar yace suna cikin murna marar misaltuwa akan nasarar da jam’iyyar su ta samu.
A ɓangaren shi Mr Mike Ojisi, Sakataren Yaɗa Labaru na Jam’iyyar PDP yace a shirye suke su sanya ƴan takarar su ga guraben ƴan majalisar, inda ya ƙara dacewa hukuncin Kotu abun ayaba ne.