An kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su bayan wani artabu tsakanin masu garkuwa da mutane da mafarauta a wani dajin da ke kan hanyar Okene zuwa Lokoja da kuma zuwa Abuja.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa, a ranar Talatar da ta gabata mafarauta sun kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yayin wani artabu da aka yi a dajin da ke cikin yankin Irekpeni-Osara, da ke kan titin guda, bayan da mafarautan suka afkawa maboyar barayin da ke yankin.
Daya daga cikin mafarautan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 9:12 na dare lokacin da mafarautan suka afkawa maboyar barayin da ke yankin.
Ya ce wadanda aka ceton na tafiya ne daga Lokoja zuwa Benin a lokacin da aka yi garkuwa da su a kusa da kauyen Osara, daura da babbar hanyar, inda ya kara da cewa mafarautan da suka samu kiran gaggawa, nan take suka afkawa maboyar barayin, inda suka yi ta harbe-harbe a tsakanin su.
“Abin takaici a yayin artabu da masu garkuwa da mutane, daya daga cikin biyar da aka ceto ya samu rauni a kafarsa amma an kai shi asibiti domin yi masa magani,” inji shi.
A cewarsa, wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun tsere da raunukan harbin bindiga a yayin musayar wuta da mafarautan, duk da cewa mafarautan na kan bin sahun masu garkuwar.
Shugaban karamar hukumar Okehi na jihar Kogi, Abdulraheem Ohiare, ya tabbatar da ceto mutane biyar da Yan bindigan su kayi Garkuwa da su, sun dawo gida.
Ya ce daya daga cikin biyar din da aka ceto ya samu raunin harsashi sakamakon musayar harbe-harbe da masu garkuwar, inda ya ce wanda abin ya shafa na karbar magani a wani asibiti mai zaman kansa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya, har yanzu bai samu amsa kiran waya ko amsa sakon da ya aike masa kan lamarin ba.