Mazauna jihar Imo sun fito kwansu da kwarkwata ba tare da yin la’akari da umarnin ‘zaman-gida’ da masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB suka sanya ba.
Idan za a iya tunawa gwamnan jihar, Hope Uzodinma ya baiyana cewa, ya kamata al’umar jihar su fito a yau Litinin gudanar da harkokin su na yau da kullun, batare da tsoro ba, inda kuma yayi ikirarin kare su daga barazanar tsaro.
Idan za’a iya tunawa tun a watan daya gabata ne, haramtacciyar Kungiyar IPOB ta sanar da cewa, ta Sanya dokar ‘zama-a-gida’ a duk ranar Litinin, a daukacin Kudu maso Gabashin kasar nan, don nuna rashin amince wa da ci gaba da tsare Shugaban ta Mazi Nnamdi Kanu.
Kazalika Kungiyar ta kuma yi barazanar nuna fishin ta ga mazauna yankin da suka Saba dokar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya waicin aiyukan Mazabu na Gwamnatin Tarayya a Yobe, a takadda kawai suke
Sai dai tun bayan ziyarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Kai jihar Imo a makon da ya gabata, Gwamnan jihar Hope Uzodinma, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro sun kawo karshen barazanar kungiyar ta IPOB, bayyan wasu tohuna da majiyar jaridar Dimokuradiyya ta samu, Kuma a ka dauke su a Owerri babban birnin jihar.
Comments 1