By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Bayelsa ta sanya dokar hana fita daga magariba har zuwa wayewar gari a kan hanyoyin ruwan ta a matsayin wani mataki na dakile fashin teku, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Dokar hana zirga -zirgar ruwan tana farawa ne daga karfe 7 na dare har zuwa karfe 6 na safe Gwamnatin ta kuma sanya dokar hana amfani da kwale-kwale mai karfin doki 200.
An sanar da waɗannan matakan a daren ranar Litinin a Yenagoa a ƙarshen taron Kwamitin Tsaro na Jiha wanda Gwamna Douye Diri ya jagoranta a Gidan Gwamnati.
Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro na I, Mista Akpoebi Agberebi, yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani kan sakamakon taron yace, daga yanzu, ba za a ba da izinin yin amfani da injinan masu karfin dawakai 200 ba, yana mai gargadin cewa masu karya doka zasu fuskanci cikakken fushin doka.
Amma, yace za a sami rangwamen motsi na gaggawa yayin awanni na dokar hana fita suka wuce inda ya yi kira ga mazaina Bayelsa dasu kai rahoton duk abinda basu yarda dashi ba zuwa ga jami’an tsaro na jihar, Operation Doo-Akpo, kan layukan wayoyin da aka bayar.
Agberebi ya kuma ce majalisar ta yanke shawarar cewa al’ummomin da gwamnatin jihar ta mallaki filayen su, su guji duk wani nau’in zanga -zanga.
Tun da farko a cikin tuhumar sa ga sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Benjamin Okolo, Gwamna Diri ya bayyana kyakkyawan fata a gareshi, sannan yana fatan zai kara wa jihar daraja ta hanyar dakile aikata laifuka.
Diri ya bukaci sabon shugaban ‘yan sandan da ya hada karfi da karfe tare da hadin gwiwar hukumomin tsaron jihar musamman don kawar da aikata munanan dabi’u a cikin jihar.