A ci gaba da buga gasar kwallon kafa ta kofin zakarun Turai, a daren jiya Juma’a ne Bayern Munich dake Jamus ta keta haddin Barcelona ta Sipaniya a gasar dab da na kusa da karshe, inda Bayern Munich din ta zazzagawa Barcelona ci 8 da 2.
Lamarin dai ya girgiza magoya bayan Barcelona. Wanda kuma wannan nasarar da Bayern Munich ta samu ya ciccidata zuwa wasan dab da na karshe, inda zata kata kara da Lyon ko Manchester City, wanda kuma kungiyoyin biyu za su kara da juna a yau.
Duk wacce ta samu nasara, za ta buga ne da Bayern Munich.
A bangare guda kuma, PSG za ta kara wasan dab da na karshe tsakaninta da Leipzig dake kasar Jamus bayan Leipzig din ta doke Athletico Madrid da ci 2 da 1, inda su kuma PSG suka doke Atlanta da ci 2 da 0 a wasan da suka buga a ranekun Laraba da Alhamis.