A gasar zakarun Turai na kakar wasa na bana da aka fara a daren yau Talata, kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich daga Jamus ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daga Sipaniya.
Gasar wanda aka hada kungiyoyin biyu a rukuni daya an buga shi ne a daren yau, inda Bayern Munich ta yi wa Barcelona ligi-ligi da ci 3 da nema.
Muller shi ne wanda ya fara zurawa Barcelona kwallo a raga a minti 34, inda a haka aka tafi hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo ne, Lewandoski ya zura kwallo ta biyu a minti na 56, inda kuma a minti na 85 ya zura kwallo ta uku.
Tsawon mintina 90 da aka buga a wasan na daren yau, mai tsaron gidan Bayern Munich, Nuer bai kama kwallo ko daya da hannunsa ba sakamakon Barcelona ba ta kai wani hari mai hatsari ba.