Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a jiya Asabar ya ce jam’iyyar ba za ta iya tilasta wa kowane dan majalisa tsayawa ko ficewa ba.
Abdullahi Adamu Ya bayyana haka ne bayan ya ziyarci gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule a gidan gwamnati dake Lafia.
“Ba za mu so mu rasa wani memba ba amma idan mamba yana son barin jam’iyyar ba tare da neman mafita ba, ba za mu iya tilasta kowa ya zauna ko barin jam’iyyar ba,” in ji shi.
“Batun sauya sheka, akwai lokacinsa a siyasa musamman a kasashe masu tasowa, kuma ba labari bane a Najeriya.
“Duk wanda yake cikin wannan jam’iyya babba ne kuma idan babba ya yanke shawara, to ko dai ka gamsar da shi, idan kuma hukuncin bai yi maka dadi ba kuma ya aikata abin da ya umarce shi, ka bar shi ga Allah shi ne ya tsara komai.
A cewar Shugaban jam’iyyar APC, jam’iyya mai mulki za ta ci gaba da samun nasara a zaben 2023 duk da rigingimun cikin gida da take fama da su.
Ya bayyana cewa sauya shekar da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi zuwa wasu jam’iyyun siyasa ba zai hana jam’iyyar tabbatuwa da mayar da hankali ba.
“Da yardar Allah za mu ci zabe, Za mu yi aiki kamar shi ne zaben karshe da za mu gudanar,” Adamu ya kara da cewa.