Shugaban Hukumar Hana sha da Fataucin miyagun Ƙwayoyi na Ƙasa NDLEA Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana dalilan daya sa gwamnati bazata taɓa halasta shan wiwi a Nigeria.
Marwa yayi jawabi a wani taron lakca da Ulefunta na shekarar 2021, wanda ƙungiyar Deji ta Masarautar Akure a jahar Ondo ta shirya.
Taron Oba Aladetoyinbo Aladelusi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Chief Olu Falae suka jagoran ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Kontagora ya karɓi takardar naɗin shi daga Gwamnatin Niger
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan kafafen yaɗa labaru Femi Babafemi ya fitar, yace Marwa ya samu wakilcin Mai bashi shawara na musamman akan magance ƙwaya Otunba Lanre Ipinmisho.
Sanarwar tace “munga irin ta’addancin daya faru a ƙasashe irin su Colombia da Mexico inda aka halasta shan ƙwaya.
“Akwai manyan abubuwan dake faruwa wanda ba ƙirƙira bane, dagaske ana yin su, yadda miyagun ƙwayoyi ke yawan haifar da faɗace-fadace.
“Abun tambaya a garemu shine: Ƙwaya ta bada gagarumar gudummawa wajen kawo taɓarɓarewar tsaro a Nigeria? Tambaya itace Eh. A dalilin haka muna da dalilin dazai sanya bazamu taɓa halasta shi.