Daga: Comrd. Haruna Sardauna
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da hukuncin da majalisar zartarwa jam’iyar APC na kasa ta zartar kan cewa jihar Yobe ne zata kawo Maimaicin wanda zai maye gurbin kujerar Sakataren jam’iyar APC na kasa, kuma Shugaban, yaqi amincewa da buqatar yan wasu jihohi da suke tirjiya da kai-kawon nuna rashin adalcin sai sun kar6i kujerar Sakataren jam’iyar APC na Kasa.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya kafa hujjar kin kar6e kujerar, da cewa, kowace jiha tana da wanda yake wakiltar ta a majalisar gudanarwan jam’iyar APC, kujerar da take wakiltar jam’iyar APC a jihar Yobe, itace kujerar Sakataren jam’iyar APC na kasa, dan haka ya zama dole abar jihar Yobe ta kawo mai maye gurbin kujerar.
Hajja na Biyu, shugaba Buhari, yace dan jihar Yobe ne yaci kujerar a za6e shugabannin jam’iyar APC daya gabata a shekarar 2018, bayan ya samu nasarar lashe za6en gwamna a jihar shi, majalisar zartarwa na jam’iyar APC ta zartar da hukunci bisa adalci kan cewa, jihar Yobe zata kawo maimaicin kujerar, saboda haka ni shugaba Muhammadu Buhari, ina goyon bayan hukukuncin da majalisar zartarwar jam’iyar mu ta zartar.
Tinda majalisar zartarwar jam’iyar APC na kasa, suka zartar da hukuncin cewa, dan jihar Yobe ne zai maye gurbin kujerar Sakataren jam’iyar APC na kasa, an samu wasu ‘ya’yan jam’iyar APC daga wasu jihohi da suke nuna tirjiya na nuna rashin biyayya akan sai sun nemi kujerar, kujerar Sakataren jam’iyar APC na kasa ana bawa mai biyayya a jam’iyar ne, ba wanda suke nuna tirjiya akan hukuncin da majalisar zartarwar jam’iyar ta yanke ba.
Inaso Masu nuna tirjiya akan hukuncin da majalisar zartarwar jam’iyar APC ta yanke, ku sani cewa, jihar Yobe ta chanchanti a bata wannan kujerar saboda itace cibiyar jam’iyar APC na Najeriya, jiha daya tilo da jam’iyar PDP bata ta6a mulkar jihar ba a tarihin siyasar su, itace jihar da a za6en shugaba Muhammadu Buhari a Shekarar 2015 da 2019 ta bayar da kuri’u mafi girman Kaso a tsakanin jihohin Najeriya 36 da Abuja burnin tarayya.
A za6en shekarar 2019, sakamakon za6en jihar Yobe saida ya haifar da cece-kuce tsakanin jam’iyar Adawa ta PDP da jam’iyar APC a dakin kar6an sakamakon za6eb Hukumar INEC, jiga-jigan jam’iyar PDP sun zayyana cewa ba za6e akayi a jihar Yobe ba saboda yawan kason da talakawan jihar suka bayar a Shugaba Buhari, anyi amfani da Kuri’un jihar Yobe an biya bashin jihohin Inyamurai 4 a Kudancin Najeriya.
Saboda haka mararsa biyayyar da suke nuna tirjiya akan hukuncin da majalisar zartarwa jam’iyar APC ta zartar, ku sani cewa ba alfarma akayi a jihar Yobe ba, jihar Yobe ta chanchanti a Kare mata hakkinta, kujerar Sakataren jam’iyar APC na kasa, hakkin jihar Yobe ne saboda dan jihar ne yaci za6en a shekarar 2018, jam’iyar APC kuma jam’iyar adalci ne, kujerar nadawa ma ta Sakataren gwamnatin kasa da aka cire dan jihar Adamawa, dan jihar aka dawo akan muqamin, balle kujerar za6e.