Bazan Daina Bugama Kasar Wales Kwallo ba, Bale
Dan wasan yace duk da Kasar Wales ta kasa samin gurbin wasan gaba bazan daina bugama kasar kwallo ba.
Yace zai cigaba da bugawa Kasar kwallo har sai lokacin da na daina wasan kwallo.
KARANTA:- Matar Gwamanan Sokoto Mairo Tambuwal ta Bukaci Yan Najeriya Dasu Dukufa Dayin Addu’a
Har yanzu dan wasan bai san matsayar sa ba fanni kwallo duba da ficewa da Kasar Wales tayi daga wasan turai bayan kasar Denmark ta lallasa su daci hudu da nema.
Dan wasan gefe na Real Madrid ya bayyana kudrin sa akan yin kwallo a kasar wale amma sai dai bai ambata ba saboda zai yawo cecekuce.
A lokacin da ake zantawa dashi kamin wasan su day kasar Denmark ake tambayar sa ko wannan ne wasan ka na karshe?
Sai yace wannan tambayar banzan an dade ana yiman ita, zan cigaba da buga kwallo saboda ina son wasan kwallo.
Zan cigaba da bugawa Kasar Wales Kwallo har sai na daina wasan kwallo.
Yanzu na fara wasan gasar kwallo ta duniya kuma zan maida hankali akan hakan.
Nagan muna da Yan wasa kuma muna kwallo mai kyau idan muka cigaba da hakan zai bamu damar cin nasara