By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya yi Allah wadai da sace wasu ‘yan kasar China dake aiki a jihar a ranar Talata, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su rubanya kokarin su ganin wadanda abin ya shafa sun dawo cikin koshin lafiya.
A wata sanarwa dauke da sa hannun babbar sakatariyar yada labaran sa Mary Noel, a ranar Alhamis a Minna, gwamnan ya bayyana damuwarsa kan jajircewar da ‘yan ta’addan suka nuna na kai wa ma’aikatan hari a gaban jami’an tsaro da ke aiki a wurin da suke aiki.
Ya kuma jaddada bukatar jami’an tsaro su mayar da ayyukan ta’addanci a wasu sassan jihar zuwa mataki mafi karanci, musamman a yanzu da gwamnatin tarayya ta ayyana masu aikata laifin a matsayin ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa sace sacen zai haifar da koma baya ga isar da ayyukan da ake gudanarwa.
“Harin yana da matukar tayar da hankali domin zai haifar da koma baya ga aikin madatsar ruwa ta Zungeru, wanda gwamnatin tarayya ta yi kokarin kammalawa cikin lokaci,” in ji Bello.
Sannan ya bayyana bakin cikinsa kan asarar rayuka da aka yi a lokacin sace ‘yan Chanan, ya kuma kara da cewa wannan lamari ne mara dadi da bai kamata ya sake faruwa a jihar ba.
Gwamnan ya kara da cewa, “Na yi matukar bakin ciki da jin wannan harin. Ya ma fi damuwa sanin cewa an shiga cikin rayuwar ma’aikata. Wannan matakin na iya yin illa ga kammala aikin madatsar ruwa ta Zungeru, wanda ke da matukar muhimmanci ga kasar.
“Zuciyata na tafe da iyalan ma’aikatan da aka sace da wadanda suka jikkata; Ina rokon Allah Ya ba su lafiya cikin gaggawa.”